Abin da ban haushi, ban tube takalmana ba Paul Pogba ya ce bai yi ritaya ba

September 2024 · 2 minute read

-‘Dan kwallon Man United, Paul Pogba ya ce bai yi ritaya a kasarsa ba

-Ana rade-radin cewa ‘Dan kwallon zai daina buga wa kasar Faransa

-Pogba ya zai kai 'Yan jarida kotu a kan wannan labari na soki-burutsu

‘Dan wasan tsakiyan kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya fitar da jama’a daga duhu a kan rade-radin da ake yi cewa ya ajiye kwallo a gida.

A ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2020, ‘dan wasan ya musanya rade-radin da ya ke yawo cewa kalaman Emmanuel Macron sun sa ya yi ritaya.

“Ba za ta sabu ba.” ‘Dan wasan mai shekara 27 a Duniya ya rubuta a shafinsa na Twitter jiya.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya raba jiha da kungiyar Kasar Saudi

Pogba ya karyata wannan labari a dandalin sada zumunta, ya kira rahoton da labarin bogi, kunshe da hoton kanun wannan labari da ke yawo.

“To …. (Jarida) ta sake yin abin da ta yi kenan. Shakka babu 100% na labarin bogi maras tushe, a je ana fadin abin da ban fada ba, kuma ban yi tunani ba.”

‘Dan wasan ya koka da yadda ake amfani da shi da kungiyar kwallon Faransa wajen karya.

“Ina bakin ciki, fushi da mamakin yadda wasu ‘gidajen yada labarai; za su yi amfani da ni, su buga labaran karya a lamarin da ya shafi halin kasar Faransa.”

KU KARANTA: Kalaman shugaba Macron sun sa Pogba ya ajiye kwallo a gida

“Ba na goyon bayan duk wani irin ta’addanci da tada rikici. Abin takaici wasu gidajen jaridu ba su yin abin da ya dace wajen buga labarai.” Inji Paul Pogba.

Pogba ya yi barazanar shiga kotu da wadanda su ka buga wannan labari ba tare da tantance wa ba.

Mu na cikin wadanda su ka kawo labari cewa Paul Pogba ya yi ritaya daga Faransa a dalilin zargin Musulunci da ta’addanci da Emmanuel Macron ya yi.

Inda mu ka yi kuskuren shi ne mun dogara da rahotanni da su ka fito daga gabas ta tsakiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9knBva2tnYq6jtc1mm5plkpa7brTArqqhoV2Xrq95066ZnmWklriiuMyapZplkpZ6sa3UpWSpp5eXrm7FwGaanmWSlrZuxchmqaKska6ubq7AZ5%2BtpZw%3D